Cocin TB Joshua zai amsa tambayoyi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Galibin wadanda suka mutu a ginin cocin TB Joshua 'yan Afrika ta Kudu

Jami'in gwamnati mai binciken musabbabin mutuwa a Nigeria ya yanke hukuncin cewar ya kamata a gurfanar da babban Cocin nan da wani fitaccen mai wa'azi TB Joshua ke tafiyarwa gaban kuliya.

Daya daga cikin gine-ginen cocin ya fadi a bara, inda ya kashe mutane 116.

Galibin wadanda suka mutu din dai yan kasar Afrika ta Kudu ne.

Jami'in ya ce cocin bai samu izinin da ya kamata kafin ya gina wani gidan baki mai bene hawa da yawa ba.

Ya ce ya kamata a binciki wadanda suka gina gidan bakin.

TB Joshua ya dora alhakin hadarin na bara a kan wani karamin jirgin sama wanda ya ce yayi ta zagayen ginin.