TB Joshua ya yi watsi da hukuncin kotu

Image caption TB Joshua na da farinji a tsakanin Kiristoci

Cocin fitaccen mai wa'azin nan TB Joshua ya yi watsi da hukuncin da wata kotu ta bayar cewa za a iya gurfanar da shi domin amsa tuhuma game da wani ginin sa da ya ruguje a bara wanda ya hallaka mutane dari da goma sha shida.

Cocin ya bayyana hukuncin da cewa babu adalci a cikinsa kuma ya karkata ga bangare guda.

Ya nanata matsayinsa cewa rushewar gidan saukar bakin na cocin da ke tsakiyar birnin Lagos aiki ne na zagon kasa.

Ya danganta lamarin da wani karamin jirgin sama da ya yi shawagi ta saman ginin a lokacin.

Galibin wadanda suka mutun ya kasar Afirka ta Kudu ne.

Wasu daga cikin iyalansu sun yabi hukuncin yayin da wasu kuma suka ce aikin shaidan ne.