Tunisia za ta gina katanga tsakanin ta da Libya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Habib Essid ya ce za a gina katangar ce domin hana 'yan ta'adda tsallakawa cikin kasar.

Mahukunta a Tunisia sun ce za su gina doguwar katanga a kan iyakar kasar da Libya domin magance tsallakawar masu tayar da kayar-baya cikin kasar.

Firai Ministan Tunisia, Habib Essid, ya ce katangar za ta kai tsawon kilomita 160 kuma za a kammala ginin a karshen shekarar 2015.

Habib Essid ya bayar da sanarwar ce a lokacin da yake jawabi a gidan talabijin na kasar a kan matakan da yake dauka domin tunkari matsalar masu tayar-da-kayar-baya bayan kisan da wani dan ta'adda da ke da alaka da kungiyar IS ya yi wa mutane 38 a birnin Sousse a watan jiya.

Ana zargin cewa dan ta'addar ya samu horo ne a wajen 'yan kungiyar ta IS daga Libya.