Wallstreet: An dakatar da hada-hada

Hakkin mallakar hoto Reuters

An dakatar da kasuwanci a kasuwar hannayen jari ta New York saboda wasu matsaloli.

Wani kakakin Kasuwar ya ce, ana aikin warware matsalolin nan ba da jimawa ba.

Ana ci gaba da hada hada a sauran kasuwannin kamar a Nasdaq.

Fadar Shugaban Amurka ta White House ta ce tana sa ido a kan lamarin.

To amma Sakataren tsaron cikin gida, Jeh Johnson ya ce, babu wata alama ta cewar matsalolin kasuwannin sun taso ne sakamakon wani kutsen tsaron internet.