'Mu muka kai hare-hare a Chadi'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Boko Haram ta kashe dubban mutane a yammacin Afirka.

Kungiyar Boko Haram ta dauki nauyin hare-haren kunar bakin wake da aka kai a birnin N'Djamena na kasar Chadi.

Kungiyar ta bayyana haka ne a shafinta na Twitter da larabci inda ta gabatar da sunaye da kuma hotunan mutane biyu da ta ce su ne suka tayar da bama baman da suka hallaka mutane 38, suka kuma jikkata sama da mutane 100.

Mazauna birnin sun ce bam din farko ya tashi ne a unguwar Dinguessou, yayin da bam na biyu ya tashi mintuna shida bayan na farko.

Mazauna birnin da dama sun shaida wa BBC cewa cikin mutanen da suka mutu har da 'yan sanda biyar.