Asusun ajiyar Nigeria ya karu — Emefiele

Babban bankin Najeriya Hakkin mallakar hoto cbn facebook page
Image caption Karuwar kudin asususun Najeriya ya faru ne saboda matakan da shugaba Muhammadu Buhari ya dauka na toshe kofofin da kudin kasar ke silalewa

Gwamnan Babban Bankin Nigeria, Godwin Emefiele ya ce ausun ajiyar kasar na kasashen waje ya karu da $2.79bn daga watan Yuni zuwa Yulin bana.

Mista Emefiele ya ce asusun ya karu daga dala biliyan 29 da miliyan 100 zuwa dala biliyan 31 da miliyan 890 a kasa da wata guda.

Ya ce an samu wannan nasara ce sakamakon matakan da sabuwar gwamnatin Muhammadu Buhari ta dauka na toshe kafofin da kudaden ke bacewa.

Gwamnan Babban bankin ya bayyana hakan ne a ziyarar da ya kai wa shugaban majalisar dattijan kasar, Sanata Bukola Saraki.

Ana sa jawabin, shugaban majalisar dattijan, Bukola Saraki, ya koka kan sakacin gwamnatin da ta gabata ta yi, a inda ta yafewa wasu kamfanoni da suke shigo da shinkafa cikin kasar biyan haraji da yawan sa ya kai naira biliyan 30.

Sanata Saraki ya kara da cewa lokacin yi wa doka karan-tsaye ya wuce a Najeriya, ya kuma yi kira ga babban bankin kasar da hukumar yaki da fasakwaurin kayayyaki su hada kai domin ganin an dawo da kudaden harajin shigo da shinkafar.