Za a fara bincike kan satar jarrabawa a Indiya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kotun Kolin ta bukaci a yi binciken kwakwaf.

Kotun Kolin Indiya ta bayar da umarni a gudanar da bincike kan gagarumin magudin jarrabawar aikin likita da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Kotun ta umarci babbar hukumar da ke bincike ta kasar -- the CBI -- ta yi binciken kwakwaf kan zargin da aka yi cewa dubban dalibai a jihar Madhya Pradesh sun biya gungun 'yan daba kudi domin su taimaka musu a wajen yin jarrabawar shiga makarantar koyon aikin likita.

Tuni aka kama kimanin mutane 2000 a kan lamarin.

Kazalika, bincike zai duba yadda mutane fiye da 30 suka mutu -- wadanda ake gani suna da alaka da batun satar jarrawar.