Yarima Saud al-Faisal ya rasu

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Margayi Yarima Saud al-Faisal

Allah ya yi wa tsohon ministan harkokin wajen Saudiyya, Yarima Saud al-Faisal rasuwa 'yan watanni bayan da aka maye gurbinsa bayan shafe shekaru arba'in a kan mukamin.

Ya rasu yana da shekaru saba'in da biyar.

Kasancewar sa wanda ya fi dadewa a mukamin ministan harkokin waje, Yarima Saud ya yi suna a fagen siyasar duniya.

A zamanin rayuwarsa yarima Saud ya ce babban bakin cikinsa shine yadda shugabannin larabawa suka kasa cimma burin kafa kasar Falasdinawa.