EFCC ta gurfanar da Sule Lamido a kotu

Image caption Ana zargin Sule Lamido da yin facaka da kudaden jihar Jigawa.

Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin aziki zagon ƙasa a Najeriya, EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Jigawa tare da 'ya'yansa biyu a gaban kuliya ranar Alhamis bayan ta kama shi ranar Talata.

Wakilin BBC da ke Kano ya ce Sule Lamido da 'ya'yansa sun isa kotun ne cikin raha da safiyar ranar ta Alhamis.

Ya kara da cewa an girke jami'an tsaro a ciki da kewayen kotun, ida ba a barin kowa ya shiga daga lauyoyi sai 'yan jarida.

Kakakin hukumar ta EFCC, Wilson Uwajuren, ya tabbatarwa BBC cewa an gurfanar da tsohon gwamnan a gaban kuliya ne bisa zargin sama-da-faɗi da makuden kudade a lokacin mulkinsa.

Rahotanni sun nuna cewa tsohon gwamnan da 'ya'yansa sun yi cuwa-cuwar sama da N1.3 bn.

Ko da a karshen shekarar 2012 jami'an hukumar EFCC sun kama ɗaya daga cikin 'ya 'yan tsohon gwamnan, Aminu Sule yana shirin fita kasar waje da maƙuden kuɗaɗe.