Za a tsagaita wuta a Yaman

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An hallaka mutane da dama a yakin Yemen

Majalisar dinkin duniya ta ce an cimma da yarjejeniyar tsagaita-wuta bisa dalilai na jin-kai a kasar Yaman.

Yarjejeniyar za ta fara aiki ne daga ranar Juma'a, kuma za ta ci gaba da aiki har zuwa karshen wannan watan na Ramadan.

An cimma wannan yarjejeniyar ce bayan kai gwauro-da-marin da wakilan majalisar dinkin duniya suka yi wajen shiga-tsakanin bangaren 'yan tawaye, da kuma gwamnatin Yaman.

Ana kokarin ba da damar gudanar da ayyukan jinkai ne a yankunan da ake gwabza fada.

Fiye da watanni uku kenan, da Saudiyya ta jagoranci wani kwance inda suke luguden wuta kan 'yan tawayen Houthi.

Kawancen kasashen Larabawan na goyon bayan Shugaba Abdrabbu Mansour Hadi ne.

Kawo yanzu sun kasa samun a kan 'yan tawayen.