Talakawa sun mutu wajen karbar sadaka

Hakkin mallakar hoto BBC Bangla

'Yan sanda a Bangaladesh sun ce akalla mutane 22 ne suka mutu yayin wani turmutsi a birnin Mymen-singh da ke arewacin kasar.

Lamarin ya faru ne yayin da daruruwan mutane ke kokarin kutsa kai cikin wata masana'anta inda ake raba sutura kyauta ga talakawa a matsayin sadaka

Hotunan Talabijin sun nuna inda lamarin ya auku, da kuma jinin daruruwan mutane facha- facha a kofar shiga masana'antar.

'Yan sanda sun kama mutane bakwai da suka hada da mai masana'antar.