Boko Haram ta kai hari Buni Yadi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Harin 'yan Boko Haram

Kungiyar Boko Haram ta kai hari garin Buni Yadi da ke Jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya a ranar Alhamis da dadare kuma ba a san yadda harin ya kasance ba.

Mazauna garin Damaturu sun ce sun hangi jiragen yaki suna ta shawagi a yankin.

Daman mazauna garin na Buni Yadi sun gudu tun da Boko Haram ta kwace shi kafin sojoji su fatattake su.