'Ziyara zuwa Amurka za ta yi tasiri'

Image caption Shugaba Barack Obama da Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari na Nigeria, ya bayyana cewa, ziyarar da zai kai kasar Amurka, za ta kara dankon zumunci tsakanin kasashen biyu.

Shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka, Mr Anthony Blinken ya kai masa ziyara a Abuja.

Shugaba Buhari ya shaidawa Mr Blinken cewa, Nigeria na fatan samun babban taimako daga Amurka, domin bunkasa ayyukan rundunar hadin gwiwa tsakanin kasashen tafkin Chadi, watau Multi National JTF a turance, wadda ake sa ran za ta fara aiki a karshen watan nan.

Shugaban ya kuma ce kasar sa da makwabtanta na yankin gabar tekun Guinea, za su yi maraba da karin hadin kai da Amurka, wajen inganta tsaron kan teku don kawo karshen satar mai a yankin.

A nasa bangaren, mataimakin sakataren harkokin wajen Amurkan, ya ce, ya je Abuja ne a wani bangare na shirye-shiryen ziyarar da shugaba Muhammadu Buhari zai kai wa takwaransa na Amurka, Barack Obama a ranar ashirin ga wannan watan.