Me ya sa EFCC ta dawo cikin hayyacinta?

Image caption Sule Lamido shi ne na baya bayannan da EFCC ta gurfanar

Wasu masu sharhi a harkokin siyasar Nigeria sun ce hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar ta'annati ta fara zage-dantse wajen hukunta masu laifi ne saboda ta san shugaban kasar, Muhammadu Buhari ba zai yi wasa wajen kawar da matsalar ba.

A baya dai ana zargin hukumar da jan-kafa wajen hukunta masu aikata manyan laifukan da suka shafi cin hanci da rashawa.

Sai dai tun da sabon shugaban kasar ya karbi mulki a watan Mayu, hukumar ta fara kama tsofaffin gwamnoni da jami'an gwamnati da ake zargi da cin hanci da rashawa.

Dr Jibrin Ibrahim, babban jami'i ne a Cibiyar bunkasa Dimokaradiya da ci gaba, kuma ya shaida wa BBC cewa "abin da Shugaba Buhari ya sa a gaba na farko shi ne cin hanci da rashawa, saboda haka EFCC ta fahimci cewa idan ba ta tashi tsaye ba su kansu za su samu matsala da shugaban kasa".

Ya kara da cewa akwai bukatar kara wa hukumar karfi domin ta tunkari duk wani mutum da ke da kashi-a-gindinsa.