Fashewar bututun mai ya kashe mutane 12

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wata mata ta na tafiya a kan bututun mai

Rahotanni daga Najeriya na cewar mutane 12 sun mutu sakamakon fashewar wani bututun mai a yankin Naija Delta.

Kamfanin hakar mai na Eni na kasar Italiya ya ce fashewar ya afkwu ne a kusa da wani bututun mai wanda ake gyarawa.

Kamfanin ya ce yana binciken abin da ya haddasa fashewar bututun, lamarin da ya yi sanadiyar jikkata wasu mutanen uku.

A baya dai, yankin na Naija Delta ya yi kaurin suna wajen tashe-tashen hankula.