An ceto 'yan sandan da Al-shabaab ta sace

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyar 'yan ta'adda Al-Shabab, a Somalia.

'Yan sanda a Kenya sun ce an saki jami'ansu biyu da kungiyar Al-Shabab ta sace fiye da shekaru biyu da suka gabata.

Shugaban hukumar 'yan sandan, Joseph Bonnet, ya ce an tsallaka kan iyakar kasar da jami'an biyu zuwa Somalia inda rahotanni ke cewa an yi ta yawo da su sansanonin Al-Shabab daban-daban.

Shugaban bai bayar da bayanin yadda aka sako jami'an ba, amma ya tabbatar da cewa suna cikin koshin lafiya.

Kungiyar Al-shabaab na yawan sace mutane, sannan ta kashe su bayan ta kai a kasar ta Kenya.