Shan taba yana kawo cutar tabin-hankali

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masana kiwon lafiya dai sun ce shan taba yana da matukar illa ga rayuwar dan adam.

Wani sabon bincike ya nuna cewa watakila shan taba yana taka rawa wajen wanzuwar cutar tabin-hankali.

Masu bincike na Jami'ar Kings College London, wadanda suka yi nazari kan shaidu fiye 60 game da shan taba, sun nuna cewa masu shan taba za su iya kamuwa da ciwon na tabin-hankali.

Binciken ya kuma nuna cewa sinadarin nicotine da ke cikin taba yana jirkita aikin da kwakwalwa ke yi.

Masana kiwon lafiya dai sun ce shan taba yana da matukar illa ga rayuwar dan adam.