Boko Haram: An ki bude kasuwanni a Enugu

Hakkin mallakar hoto BOKO HARAM
Image caption 'Yan kungiyar Boko Haram a Najeriya

A Najeriya, daruruwan 'yan kasuwar kudu maso gabashin kasar sun ki bude kasuwanni a wasu jihohin shiyyar a matsayin wani mataki na nuna adawa da kai wasu fursunonin Boko Haram yankin.

'Yan kasuwar sun yi dafifi a bakin kasuwar garin Ekwulobia na jihar Anambra, inda ake zargin an kai fursinonin gidan yarin garin.

'Yan kasuwar sun bayar da sanarwar rufe illahirin kasuwannin yankin na tsawon yini daya, a matsayin wani gargadi na neman a hanzarta kawar da fursunonin na Boko Haram daga gidan yarin.

Kazalika, an rufe kasuwanni a jihar Enugu, sai dai rahotanni sun nuna cewa kasuwanni sun kasance a bude a jihohin Abia da Ebonyi da Imo.

'Yan kasuwar sun ce suna jin tsoro kada 'yan boko Haram su kai musu hari idan aka ci gaba da tsare mutanen a yankin.