Harin bam ya hallaka mutane 15 a N'djamena

Dakarun kasar Chadi Hakkin mallakar hoto none
Image caption Dakarun kasar Chadi

Mutane akalla 15 ciki har da jami'an tsaro biyu ne suka hallaka a wani harin bam a babbar kasuwar N'djamena babban birnin kasar Chadi.

Wani babban jami'in 'yansanda a yankin ne ya tabbatarwa da manema labarai abkuwar lamarin.

Yace wani dan kunar bakin wake ne da yayi shigar mata ya tada bam din a daf da inda jami'an tsaro ke kula da shige da fice a kasuwar.

Kasar Chadin na cikin kasashen dake kan gaba wajen yaki da kungiyar ta Boko Haram.

Masu aiko da rahotanni sun ce kungiyar ta Boko Haram ta kara kaimin kai hare-haren a cikin wata mai tsarki na azumin watan Ramadan a kasashen Najeriya da makwabciyarta kasar Chadin.