Zazzafar muhawara a tattaunawar ceton Girka

Hakkin mallakar hoto AP

Ministan kudi na kasar Girka Euklid Tsakalotos yana neman goyon baya daga kungiyar kasashen masu amfani da kudin Euron kan bukatun baya bayan nan da kasar ta gabatar kan batun ceto ta daga rikicin bashi.

Wasu rahotanni sun ce yana samun manyan masu adawa da batun.

Akasari dai na nuna shakku game da batun--inda ministan kudi na kasar Jamus Wolfgang Schäuble ya ce shi da takwarorinsa ba za su iya sakewa da alkawuran da Girkar tayi ba.

Yayinda hakan ke faruwa ministan harkokin tattalin arziki na kasar Girka Greek Giorgos Stathakis ya shaidawa BBC cewa za a iya amincewa da gwamnatinsa wajen cika alkawuran da ta dauka saboda gwamnatin Girka da majalisar dokoki a shirye suke wajen kawo cigaba.