Firaministan Girka ya yi amai ya lashe

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Firaiministan Girka, Alexis Tsipras

'Yan majalisar dokokin kasar Girka sun amince da bukatar gwamnati ta baya bayan nan da nufin kawo karshen matsalar bashin da ta yi wa kasar katutu.

Bayan kwashe dogon lokaci ana tattaunawa a daren Asabar, 'yan majalisar dokoki 251 sun amince wa gwamnatin kasar da ta sasanta tsakaninta da masu bin ta bashi.

Sai dai kuma firaiministan kasar, Alexis Tsipras bai samu kuri'un 'yan majalisar guda 10 daga jam'iyyarsa ta Syriza ba da suka hada da ministocinsa guda biyu da kuma kakakin majalisar ta dokoki.

Alexis Tsipras dai ya bukaci da a kara wa kasar tasa bashin kudi har Yuro biliyan 53 da rabi domin cike gibin bashin da ake bin kasar zuwa shekarar 2018.

Shirin ceton kasar Girka da firaiministan kasar ya jagoranci kin amincewa da shi a makon da ya gabata, yanzu ya dawo yana neman goyon bayan 'yan majalisar kasar ruwa a jallo da su amince da shi.