An kai hari Maiduguri

Wani hari da aka kai Maiduguri.
Image caption 'Yan Boko Haram su na kara kai hare-hare a sassan arewacin Nigeria.

An kai harin kunar bakin wake Maiduguri babban birnin jihar Borno.

An kai harin kunar bakin waken ne da sanyin safiyar ranar Asabar, a kusa da ofishin jami'an tsaron farin kaya na SSS.

Wani da ya shaida lamarin ya shaidawa BBC cewa da misalin karfe 6 na safiya ne kawai suka ji karar fashewar wani abu, sun kuma yi kokarin isa wurin amma jami'an tsaro sun hana don an killace wurin.

Ya kuma Kara da cewa 'yan kunar bakin wake guda biyu ne lamarin ya rutsa da su, wadanda suka je wajen a kan Keke-napep.

Shaidu sun ce babu wani jami'in tsaro ko farar hula da ya rasa ran sa ko ya ji rauni.

Har wayau wasu 'yan gudun hijirar Nigeria da ke garin Fotokol na jamhuriyar Kamaru, sun ce mayakan Boko Haram sun yi musu kwantan bauna tare da bude musu wuta, a lokacin da suka shiga garin Gamborou dan gyara magudanar ruwa saboda faduwar da damuna ta fara yi a yankin.

Maharan sun kashe mata da maza tare da yin awon gaba da wasu matan in ji su.

Kawo yanzu dai babu wani jawabi da ya fito daga jami'an tsaron Najeriya game da hare-haren.