Ba za a bai wa Girka karin Tallafi ba- Merkel

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta yi gargadin cewa ba za a baiwa kasar Girka wani karin tallafi ceto ta daga basussuka ba .

Tana magana ne yayin da ta isa wajen taron shugabannin kasashe masu amfani da kudin bai daya na Euro a birnin Brussels

Ta ce halin da ake ciki mawuyaci ne, ta wani bangaren matsin tattalin arzikin da kasar Girka ta fada, ta wani gefen kuma rashin yarda ya shiga cikin lamarin.

Taron dai ya biyo bayan tattaunawar kwanaki biyu mai tsauri tsakanin ministocin kudi na kasashen.

Sun ce dole sai kasar Girka ta amince da sabbin dokoki zuwa ranar Laraba, wacce za ta bada damar rage yawan kudaden da take kashewa kafin a fara tattaunawa kan batun ceto tan.

Masu bada rance na kasa da kasa sun kididdige cewa kasar ta Girka na bukatar Euro biliyan 86 don kaucewa durkushewa.

Pira ministan kasar ta Girka , Alexis Tsipras ya ce a shirye yake da ya mika wuya.