Girka: An kasa cimma matsaya

Greece Hakkin mallakar hoto
Image caption Greece

Nan gaba kadan Ministocin kudin kasashen tarayyar turai za su koma kan teburin tattaunawar da suke tare da takwaransu na Girka akan batun sabuwar bukatar da Girka ta mika musu na ban-gishiri in baka manda.

An dai kwashe sa'oi 9 ba tare da cimma wata matsaya ba, lamarin da ta kai ga kasar Jamus ta yi barazanar korar Girka daga tarayyar turan amma kasashe kamar su Faransa masu tausaya wa Girkan kan irin halin da ta tsinci kanta a ciki ba su goyi bayan hakan ba.

Ministan kudin kasar ta Girka Euclid Tsakalos ya yi ta faman kokarin gamsar da takwarorinsa na sauran kasashen 27 da su amincewa shugabannin kasar tasa kan kwaskwarimar da suka ce za su yi wa tattalin arzikin Girka.

Asali ma Sun yi amanna ne da matakan tsuke bakin aljihun da kasar ta Girka ta ce za ta aiwatar idan har aka kara bashin.

Kasar ta Girka dai ta nemi da a kara mata rancen Yuro dala biliyan 80.