Za a saki mai yajin kin cin abinci a Isra'ila

Khader Adnan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Khader Adnan

Hukumomi a Isra'ila sun saki wani jagoran Falasdinawa mai fafutuka wato Khader Adnan daga gidan yari bayan amincewar da ya yi na kawo karshen yajin kin cin abinci da ya shafe kwanaki hamsin yana yi.

Ya kasance a gidan yarin tsawon shekara guda wanda kuma shine karo na 9 ana kama shi ba tare da tuhuma ba.

An dai kama shi ne bayan da aka sace tare da kashe wasu matasa Isra'ilawa 3 lamarin da ya haifar da kama wa tare da tsare Falasdinawa da dama.

Jami'an tsaron Isra'ila na zargin Mr Adnan da kasancewa dan kungiyar masu jihadi, sai dai iyalansa sun ce ba shi da hannu a dukkan wasu ayyukan masu tayar da kayar baya.