Ana artabu a lardin Anbar na Iraki

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kungiyar IS ce keda iko da lardin Anbar

Sojojin Iraki sun ce sun kai farmaki da nufin fattakar mayakan IS daga lardin Anbar.

Sun dai yi wannan sanarwar ce ta gidan Talabijin, suna cewa rundunarsu za ta kunshi sojoji da kawancen mayakan 'yan shi'a da kuma kabilun yankin.

Birgediya-Janar Yahya Rasoul Abdullah shi ne ya yi sanarwar "Ya kun 'ya'yan wannan kasa ta Iraki mai daraja, da taimakon Allah, an kaddamar da hare-hare da misalin karfe 5:00 na safe da nufin kwato Anbar."

Babu dai cikakken bayani a kan farmakin, amma an yi amanna cewa sojojin Irakin za su mai da hankali ne wajen kai hari kan Fallujah.

Masu aiko wa BBC rahotanni dai sun ce sojojin Irakin sun dade suna yunkurin kwace iko da Anbar daga hannun IS, amma har yanzu ba su yi galaba ba.