Buhari ya nada sababbin jami'an tsaro

Hakkin mallakar hoto Nigeria Govt
Image caption Buhari ya gana da sabobbin manyan jami'an tsaro

Shugaba Muhammadu Buhari na Nigeria ya amince da nadin sababbin manyan jami'an tsaron kasar.

A cikin wata sanarwa da kakakin shugaban kasar, Femi Adesina ya fitar, ta ce an nada Manjo Janar Abayomi Gabriel Olonishakin a matsayin babban hafsan hafsoshin tsaron kasar.

Sai kuma Manjo Janar Tukur Yusuf Buratai a matsayin hafsan dakarun sojin kasa na kasar.

Sanarwar ta ce sabon hafsan dakarun sojin ruwan kasar shi ne Rear Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas a yayinda aka nada Air Vice Marshal Sadique Abubakar a matsayin babban hafsan sojin saman kasar.

Sauran wadanda shugaba Buhari ya nada a bangaren tsaron, sun hada da Air Vice Marshal Monday Riku Morgan a matsayin babban jami'in kula da bayanan sirri na tsaro a kasar da kuma Manjo Janar Babagana Monguno a matsayin mai bai wa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro.

'Kora'

A ranar Litinin ne aka sanar da korar manyan jami'an tsaron kasar a wani mataki da ake kallo na yunkurin Shugaba Buhari na yaki da kungiyar Boko Haram.

Wadanda aka kora su ne: Air Marshal Alex Badeh, Janar Kenneth Minima da Rear Admiral Usman Jibrin da kuma Air Vice Marshal Adesola Amosun.

An dade ana saran shugaba Buhari zai kori manyan hafsoshin tsaron a daidai lokacin da kungiyar Boko Haram ke ci gaba da kaddamar da hare-hare a cikin kasar.

A cikin kwanaki goma da suka wuce an kashe mutane fiye da 220 a Nigeria sakamakon hare-haren Boko Haram.

Hakkin mallakar hoto Nigeria State House
Image caption Sabobbin manyan jami'an tsaron Nigeria