Likita a Ghana zai sha daurin shekaru 25

Hakkin mallakar hoto KOMLA KLUTSE
Image caption Lauyoyin Dr Sulley sun ce za su daukaka kara

A yanke wa wani likita a kasar Ghana hukuncin daurin shekaru 25 a gidan yari saboda lalata da wani yaro matashi dan shekaru 15.

An samu Dr Sulley Ali-Gabass wanda ke aiki a asibitin Effia Nkwanta da ke garin Takoradi da laifin yin lalata da yaron wanda aka gano yana dauke da kwayar cutar HIV.

Lauyoyinsa sun ce za su daukaka kara.

A cewar Lauyoyin, Likitan ba ya dauke da kwayar cutar HIV a don haka babu yadda za a ce shi ne ya yada cutar a kan matashin.