Tsipras ya bada kai bori ya hau

Firaministan Girka Alexis Tsipras Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Firaministan Girka Alexis Tsipras

A na ci gaba da taron gaggawa na shugabannin kasashen tarayyar turai a Brussels domin samar da matsaya da za ta kange Girka daga fadawa kangin talauci sannan kuma ta ci gaba da amfani da kudin bai-daya na tarayyar turan.

Yanzu haka dai firaiministan kasar ta Girka, Alexis Tsipras ya damu kwarai da aniya wajen ganin an lalubo mafita tun kafin bankunan kasar su durkushe.

An ce shugabannin dai suna tunanin shirya wani daftari na shida kan sauye-sauyen da suke son kasar ta Girka ta aiwatar kafin su lamince a ceci ta.

Kusan za a iya cewa wannan shi ne karo na farko da maitar firaiministan Girka, Alexis Tsipras kan shirin ceton kasarsa ta fara fitowa fili.

Domin kuwa ya yi matukar matsuwa da a cimma matsaya kafin bankunan kasar su fada yanayin talauci.

Sai dai su kuma shugabannin kasashen tarayyar turai sun ce za a kara tallafawa kasar ta Girka ne bisa sharadin samun tabbacin aiwatar da sharuddan da tarayyar za ta gindaya mata.