Za a bai wa Girka karin bashi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Alexis Tsipras ya ce kasarsa ta jajirce sosai kan biyan bashin, yana mai cewa suna fuskantar mawuyacin zabi.

Shugabannin Tarayyar sun amince su bai wa kasar Girka bashi a karo na uku bayan wani taro da suka yi Brussels.

Shugaban majalisar Turai, Donald Tusk, ya ce sun tsara duk hanyoyin da za a yi garambawul da kuma taimaka wa Girka da kudade.

Yanzu dai dole Girka ta aiwatar shurudan da aka gindaya mata -- cikin su har da kara haraji ga 'yan kasar da rage kudin fansho da yin gyara ga dokokin ma'aikata na kasar da kuma samar da asusun da za a ajiye kudaden da za a biya bashi da su.

Idan kasar ta aiwatar da wadannan sharuda, to za a ba ta kimanin $95bn a cikin shekaru uku.

Firai Ministan kasar, Alexis Tsipras ya ce kasarsa ta jajirce sosai kan biyan bashin, yana mai cewa daga karshe dai suna fuskantar mawuyacin zabi.