Joaquin Guzman ya tsere daga gidan yari

Joaquin Guzman Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Joaquin Guzman

Mahukunta a Mexico sun kaddamar da gagarumin shirin farautar daya daga cikin manyan masu fataucin miyagun kwayoyi joaquin Guzman bayan ya tsere daga wani gidan yari mai tsatstsauran tsaro.

An dai ga jirage masu saukar ungulu na shawagi a saman gidan yarin da aka tsare da mutumin, yayinda aka dakatar da tashin jiragen sama na wucin gadi daga filin saukar jiragen saman dake kusa da gidan yarin.

An dai tuhumi ma'aikatan gidan yarin bayan da aka fuskanci ya yi kokari ya tsere.

Shugaban kasar Mexico Enrique Pena Nieto ya ce yana so a gudanar da cikakken bincike akan tserewar Mr Guzman.

Ya ce ya bawa ofishin Attorney janar umarnin gudanar da cikakken bincike domin gano ko akwai hannun ma'aikatan gidan yarin a tserewar mutumin.