An aiwatar da hukuncin kisa a Abu Dhabi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Babbar kotun shar'ia ta China.

Hukumomi a tarayyar Daular Larabawa sun aiwatar da hukuncin kisa kan wata matar da ta kashe wata malamar makaranta 'yar Amurka.

Matar ta soka wa malamar mai suna Ibolya Ryan wuka ne a wani bandakin da ke wata cibiyar cinikayya a tsibirin Reem.

An kuma samun Alaa Badr Abdallah da laifin dasa bam a wajen wani gida a birnin Abu Dhabi a ranar, inda aka kwance shi.

Babbar kotun kasar ta yanke mata hukuncin kisa, kuma an aiwatar da hukuncin duk da cewa ba a cika zartar da hukuncin kisa a Daular Larabawan ba.