Yi wa dokokin wa'adin mulki karan tsaye

Hakkin mallakar hoto Nkurunziza
Image caption Shugaba Pierre Nkurunziza is yana takarar neman zaben shugaban kasar da za ayi a Burundi a 15 ga watan Yuli.

Duniya a yanzu ta tara shugabannin kasashen da ba su son mika ragamar mulkin kasashen su.

Misalin shugabanni irin haka shi ne a kasar Burundi, inda shugaba Pierre Nkurunziza ya ke yakin neman a sake zaben sa karo na uku, duk kuwa da tashin hankalin da masu adawa da burin na sa suka tayar cewar wa'adin mulki biyu kawai zai yi.

Shugaba Nkurunziza dai ya hau kujerar na ki, yana cewa tun da ba jama'a ne suka zabe shi a karo na farko ba, saboda haka babu shi a lissafi.

Jama'a da dama suna zargin cewar Shugaban Rwanda wanda ke makwabtaka da Burundi, Paul Kagame, shi ma yana neman wuce lokacin mulkinsa na biyu.

Babu dai wanda ya kai ga babakeren Shugaban Gambia, Yahya Jammeh wanda ya shaida wa BBC a shekarar 2011 cewa, "idan ma zan iya shekaru biliyan ina mulki, toh zan yi".

Mulkin dole ba ya dorewa

An hambarar da shugaban kasar Burkina Faso, Blaise Compaore saboda yunkurin sa na neman canza kundun tsarin mulkin kasar domin neman a sake zaben sa.

Tazarce

Wasu shugabannin na neman bin doka wurin yakin neman zaben, wasu kuma suna yi wa doka karan tsaye.

A farkon shekarar nan a wani taron Kungiyar tarayyar Afrika, Shugaba Robert Mugabe ya ce "gaskiya an shake wuyar shugabanni, idan har an ce sai dai su yi mulki shekaru biyu kacal".

Shugaba Mugabe ya kara da cewa, "Ai dimokradiyya ce, idan jama'a sun bukaci shugaba ya ci gaba, toh a bar shi ya ci gaba mana."

Wasu cikin shugabannin kasashen gabashin Asiya ma haka suke shafa shekaru da dama suna mulki duk kuwa da kasashen sun samu 'yancin kansu.

Shugaban kasar Indonesia ya shafe shekaru 22 a kan mulki, yayin da shugaban Singapore, Lee Kuan Yew ya yi Firayi minista tun shekarar 1959 zuwa shekarar 1990.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Lee Kuan Yew ya dade yana mulkin Singapore, amma ya kawo masu cigaba matuka a kasar.

"Lee Kuan Yew mutum ne da ya fita daban da saura, bayan kuma ya sauka daga mulki tattalin arzikin kasar ya karu sosai a kan yadda ya tarar da shi." In ji Farfesa Kishore Mahbubani daga jami'ar Lee Kuan Yew School of Public Policy na Singapore.

Ana yi wa mulki sau biyu kallon dab'iar nasara, saboda daukacin shugabannin Amurka sau biyu su ke yi.

Alamun cutar 'Hubris'

Masu neman a tsawaitawa shugabanni adadin mulki suna ganin dadewa a kan karagar mulki kan janyo sauyi a halayya da kuma yadda zai rika yanke hukunci.

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Lord Owen ya jagoranci jami'iyyar led the Social Democratic Party ta Amurka a shekarar 1980.

Tsohon sakataren harkokin wajen Biritaniya kuma likitan masu tabin hankali, Lord Owen ya yi bayanin dadewa a kan mulki yana sa wasu shugabannin su zama suna da girman kai da rashin bin shawara da kuma kwarin cewa duk wani mataki da suka dauka dole ya amfani al'ummar su.

"Mulkin shekara takwas ay ya isa" In ji Lord Owen.

Barin mulki

Wani dan jarida Wilf Mbanga yana ganin Shugaba Robert Mugabe na nuna alamun cutar ta 'Hubris'.

Mbanga ya ce ya yi Robert Mugabe farin sani, kuma suna sauraron wakokin Jim Reeves tare a baya.

Ya ce "A da ina goyon bayan Mugabe da jam'iyyarsa matuka, amma yanzu gani yake Zimbabwe mallakar sa ce shi kadai".

Ana samun shugabannin da suka juya wa mulki baya.

Misali Nelson Mandela ya sauka baya wa'adin mulki daya, shi ma firayi ministan Biritaniya na yanzu David Cameron ya ce ba zai nemi a sake zabe karo na uku ba.

Cutar ta Hubris wacce tsananin son mulki ne, yana sa wasu su zauna lokuta fiye da kima inda suke mai da shi tamkar gado, kuma su kasa su tsare har tsufansu.