Za a iya kawar da AIDS zuwa 2030 - Ki Moon

Image caption Ban Ki Moon, Sakatare janar na majalisar dinkin duniya

Sakatare Janar na Majalisar dinkin duniya, Ban Ki Moon ya ce duniya ta yi nasarar cin karfin cutar AIDS ko CIDA, a yakin da ake yi da annobar.

Mr Ban Ki Moon ya bayyana haka ne a Addis Ababa, babban birnin Habasha, lokacin da ake gabatar da rahoton shekara-shekara a kan yakin da ake yi da cutar.

Majalisar Dinkin duniyar dai ta ce yaduwar da cutar AIDS ke yi ta ragu da kashi 35 bisa dari, kuma an cimma burin da ake da shi na yi wa mutum miliyon 15 masu fama da cutar jinya nan da karshen wannan shekara:

Wakiliyar BBC ta ce sama da mutum miliyon 15 ke nisan-kwana sakamakon amfani da maganin kashe kaifin AIDS ko kanjamau.

Majalisar dinkin duniyar ta ce idan aka tsaya tsayin-daka za a iya kawar da annobar nan da shekara ta 2030.