An bukaci jami'an tsaro su dawo da kimar Nigeria

Hakkin mallakar hoto Nigeria Govt
Image caption Buhari ya ce akwai bukatar manyan jami'an tsaron su mai do da kimar Najeriya.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci sababbin manyan jami'an tsaro su mayar da kimar kasar a idanun duniya.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a ganawar da ya yi da jami'an tsaron jim kadan bayan ya nada su ranar Litinin.

Muhammadu Buhari ya ce kimar kasar ta zube a idanun duniya saboda yadda 'yan boko Haram suke kai hare-hare babu kakkautawa da kuma gazawar jami'an tsaro wajen magance matsalar.

Ya kara da cewa Najeriya tana da duk wata dama ta iya murkushe 'yan ta'adda, yana mai cewa akwai bukatar manyan jami'an tsaro su zage-dantse wajen kawar da masu tayar-da-kayar-bayan.

Mutanen da aka nada a kan sababbin mukaman su ne: Manjo Janar Abayomi Gabriel Olonishakin a matsayin babban hafsan hafsoshin tsaron kasar.

Sai kuma Manjo Janar Tukur Yusuf Buratai a matsayin hafsan dakarun sojin kasa na kasar.

Kazalika an nada Rear Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas a matsayin hafsan dakarun sojin ruwan a yayin da aka nada Air Vice Marshal Sadique Abubakar a matsayin babban hafsan sojin saman kasar.

Sauran wadanda shugaba Buhari ya nada a bangaren tsaron, sun hada da Air Vice Marshal Monday Riku Morgan a matsayin babban jami'in kula da bayanan sirri na tsaro a kasar da kuma Manjo Janar Babagana Monguno a matsayin mai bai wa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro.