An damke tsohuwa 'yar Boko Haram a Kamaru

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun Kamaru sun ce za su kawar da Boko Haram

Hukumomi a Kamaru sun damke wata tsohuwa bisa kokarin yin kunar bakin wake a kusa da wani cocin 'yan katolika.

An damke dattijuwar ce a Kousseri inda ta yi shigar mabarata domin bad-da-kama.

A yanzu dai hukumomin tsaron Kamaru sun zage damtse tun bayan da aka samu harin kunar bakin wake na farko a kasar a karshen mako a Fotokol.

Tuni aka haramta saka nikabi a wani matakin dakile wadanda ke aikata kunar bakin wake.

'Yan Boko Haram sun janyo tabarbarewar tsaro a Kamaru, da Nigeria, da Niger, da kuma Chadi lamarin da ya janyo mutuwar dubban mutane.