An damke wani bisa zargin fyade a Kaduna

Image caption Ana zargin wani mutum da yi wa wani yaro dan shekaru 9 fyade.

Rundunar 'yan sanda a jihar Kaduna da ke arewacin Nigeria ta tabbatar da kama wani mutum wanda ake zargi da yi wa yaro dan shekaru 9 fyade.

Ana zargin mutumin da aka kama a unguwar Malali, da yi wa wannan yaro fyade a lokuta da dama, har zuwa ranar da dubun sa ta cika.

Wata kungiya mai fafutukar kare hakkokin mata da yara kananan ce ta shigar kira a kan wannan batu, inda ta ke kokarin ganin an gudanar da sahihin bincike domin kwatowa yaron hakkin sa.

Mahaifin yaron ya shaida wa BBC cewa, yaron ya bayyana mata cewa wannan karo na biyar kenan ana masa fyaden, kuma suna tare shi ne kan hanyar sa ta zuwa makarantar Islamiyya.

Ambassada Amina Usman ta kungiyar masu fafutukar kare hakkin mata da kananan yara ta ce "An kai yaron wurin likita inda aka same shi da raunuka matuka sakamakon fyaden".