Mutane uku sun mutu saboda sadaka a Kaduna

Image caption Turmutsutsu ne ya jawo asarar rayukan

A kalla mutane uku ne suka rasa ransu, wasu da dama kuma suka jikkata sakamakon turmutsutsu da aka yi lokacin karbar sadaka a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya.

Bayanai dai sun ce jama'a da dama da suka hada da nakasassu da mutanen gari ne suka hallara yayin da ake raba sadakar a gidan wani mai-hannu-da-shuni a jihar.

Mutanen da ke karbar sadakar sun ce mutumin ya saba bayar da ita a duk shekara cikin kwanciyar hankali sabanin ta bana.

Wasu sun alakanta dalilin mutuwar mutanen da sanya ranar karbar sadakar ta zamo daya ga maza da mata abin da ya kawo turmutsutsu, sabanin a baya a inda a kan sanya ranakun karbar sadakar daban-daban ga jinsin guda biyu.

Yanzu dai hukumomi sun dakatar da mai-hannu-da-shunin daga raba sadakar har sai an ga yiwuwar ci gaba da ita.