Kotu ta ba da belin Sule Lamido

Image caption Efcc ce ta kama Sule Lamido da 'ya'yansa

Babbar kotun tarraya da ke Abuja ta ba da belin tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido wanda ke zaman kurkuku tun a makon da ya gabata.

Hukumar EFCC ce ta shigar da kara a kansa bisa zargin almundahana da kudaden al'umma a lokacin ya na mulkin jihar ta Jigawa.

An damke tsohon gwamnan ne da 'ya'yansa maza biyu inda aka tsare su a gidan yari na Kurmawa a Kano kafin a kai su gidan yari na Kuje da ke Abuja.

Rahotanni sun nuna cewa tsohon gwamnan da 'ya'yansa sun yi cuwa-cuwar sama da N1.3 bn.

Ko da a karshen shekarar 2012 jami'an hukumar EFCC sun kama daya daga cikin 'ya 'yan tsohon gwamnan, Aminu Sule yana shirin fita kasar waje da makuden kudade.