Yarjejeniyar Girka ba za ta yi aiki ba- IMF

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Girka na cikin mawuyacin hali

Assusun bayarda Lamuni ta duniya IMF ya yi kakkausar suka ga sharuddan yarjejeniyar ceto tattalin arziki wanda tace nahiyar Turai ta kakaba akan Girka

Wani jami'in IMF ya ce sauye -sauyen da ake tsammanin ganin Girkan ta yi, abune da ba zai taba yiwuwa ba

IMF ta ce idan ma Girkan ta aiwatar da cikakken shirin matakan tsuke bakin aljihun, ba za ta iya biyan bashin biliyoyin kudaden euro da masu bata bashi ke bin ta ba

Don haka IMF ta ce Girka fa na bukatar a saukaka mata bashin da ake bin ta ne, fiye da yadda Turai take dauka.

Wani wakilin BBC kan tattalin arziki ya ce sa-bakin da IMF ta yi, zai sa Firai Ministan Girka ya sha wahala wajen rarrashin 'yan majalisar dokokin kasar a Athens, wajen ganin ya samu goyan bayansu ga matakan tsuke bakin aljihun da masu baiwa kasar bashi na nahiyar Turai suke bukata daga kasar