Obama ya nemi a yi kwaskarima ga bangaren shari'a

Hakkin mallakar hoto
Image caption Tsarin yiwa masu laifi shari'a a Amurka na jefa bakaken fata da dama a gidajen yari

Shugaba Obama ya yi kira da a gudanar da wani gagarumin sauyi a tsarin yiwa masu aikata laifi shari'a na kasar

Ya ce hukuncin da ake yankewa a shari'oi da dama nada tsauri sosai, kuma ladabtarwar da ake yi wa masu laifi, ba ta dacewa da irin laifin da suka aikata.

Mr Obama ya sanar da cewa gwamnati zata sake duba yadda ake amfani da tsarin nan, na kebe fursunoni a wani waje, sannan da hana su ganawa da iyalai da kuma 'yan-uwa.

Sannan ya na bukatar majalisar dokoki ta amince da wani kudurin sauyi na hukunci zuwa karshen shekara.