Za mu yi sulhu da gwamnati— Mullah Omar

Image caption Shugaban Taliban, Mullah Omar

Jagoran kungiyar Taliban, Mullah Omar ya nuna goyon bayansa ga shirin tattaunawar sulhu da gwamnati.

A wani sakon taya al'umar Musulmi murnar Sallar Azumi da ba kasafai yakan yi ba, jagoran ya ce addinin Musulunci bai hana mu'amala da abokan gaba ba.

Mullah Umar ya ce tattaunawar sulhun ma za ta taimaka wajen kawo karshen sojojin kasashen waje da suka mamaye musu kasa.

Sai dai bai ce komai a kan ganawar da ya yi a hukumance da wakilan gwamnatin Afghanistan a makon jiya ba, wadda kasar Pakistan ta jagoranta.