'Gwamnati ta gargadi Radio Biafra'

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Gwamnatin Nigeria ta ce ana daukar matakai na binciko tare da hukunta duk wasu da ke da hannu a wani haramtaccen gidan radio mai suna Radio Biafra da ke watsa shirye shirye a wasu yankuna na kudu maso gabashin kasar.

Haka kuma gwamnatin ta musanta wata murya da ta ce gidan rediyon ya yi ta yayatawa wanda yayi ikirarin cewa hira ce da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya yi da sashen Hausa na BBC, inda gidan rediyon ya ce Shugaba Buharin ya furta wasu kalamai da ke nuna kin jinin 'yan kabilar Igbo.

Malam Garba Shehu mataimaki na musammman ga shugaban kasa kan yada labarai,ya shaidawa BBC cewa ' a inda duk aka sake jin an bullo da wata tashar rediyo haramtacciya, ana yada shirye shirye na wargaza Nigeria ko wanda zai saba wa doka, gwamnati za ta dauki kwararan matakai a kan kowanene ya mallaki wannan tauraron dan-Adam din da tashar ke amfani da shi.

Garba Shehu ya kara da cewa an kira su, an kuma ja musu kunne, an ce musu su je su toshe wannan haramtaccen gidan rediyo, idan ba haka ba za su ga bacin ran gwamnatin Nigeria'.

Tabbacin da suka ba da shi ne daga ranar Laraba da daddare ba za a kara jin duriyar gidan rediyon Biafra ba' in ji Garba Shehu.