Gaskiya TV zai soma nuna shirinmu na talabijin

Hakkin mallakar hoto gaskiya tv
Image caption Ofishin Gaskiya TV a Zinder

Daga yanzu za a iya kallon shirin talabijin na sashin Hausa na BBC a gidan talabijin na Gaskiya da ke Zinder a Jamhuriyar Nijar.

Gaskiya TV zai dinga nuna shirin talabijin din na tsawon mintuna 10 daga karfe tara na dare, daga ranar Litinin zuwa Juma'a.

Gidan talabijin na Gaskiya shi ne mafi girma a yankin Zinder.

Editan sashin Hausa na BBC, Mansur Liman ya ce "Mun ji dadin wannan kawancen. Muna sa ran al'ummar Zinder za su dinga kallon shirye-shiryenmu."

Manajan Darektan Gaskiya Talabijin, Binia Malam Lawali ya ce "Muna alfahari da wannan kawance na kasancewa tasha ta farko da za ta nuna shirin talabijin na BBC a Zinder."

A watan Samtubar 2014 ne sashin Hausa na BBC ya soma watsa shirin talabijin wanda ake kamawa a shafin intanet na bbchausa.com da kuma wasu tashohin talabijin a wasu kasashen Afrika.

Image caption Aichatou Moussa da Elhadji Diori Coulibaly ne ke gabatar da shirin