Mutane 50 ne suka hallaka a harin bom a Gombe

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption A watannin baya an kai harin bam a tashar Gombe line

Rahotanni daga jihar Gombe a arewacin Nijeriya na cewa adadin wadanda harin nan na tagwayen bama-bamai ya yi sanadiyar mutuwarsu da yammacin ranar Alhamis a birnin ya kai hamsin, inda a yau ake sa ran yi musu jana'iza.

Galibin wadanda suka mutu dai kananan yara ne, yayin da mutane da dama suka jikkata.

A halin da ake ciki dai, ‘yan uwa da abokan arziki na wadanda tashin bama-baman ya shafa, na ci gaba da kokarin gano ‘yan-uwansu, imma a mace ko a jikkace.

Yayin da wadanda suka gano gawawwakin ‘yan uwansu kuma ke shirin jana’iza, a daidai lokacin da al’uma ke bikin Karamar Sallah.

Hukumomi na shawaratar masu ibadar da sauran jama’a da su kara yin hattara a yankunansu.

Najeriya dai na fama da matsalar hare-haren bam da na 'yan bindiga da ke haddasa hasarar rayukan jama'a, wadanda ake zargin Boko Haram da kaiwa.