Jami'an tsaro sun dira a gidan Sambo Dasuki

Hakkin mallakar hoto The Will
Image caption Sambo Dasuki na daga cikin masu karfin fada a ji a gwamnatin da ta shude a Nigeria

Rahotanni a Najeriya sun ce jami'an hukumar tsaro ta SSS sun kai samamen ne a gidan Kanar Sambo Dasuki dake Abuja babban birnin kasar, sannan wasu jami'an hukumar kuma suka gudanar da irin wannan samame a gidan mahaifinsa dake Sokoto.

Kwanaki hudu kenan da sauke Kanar Sambo Dasuki daga mukamin mai bai wa gwamnatin Najeriya shawara kan sha'anin tsaro, ya bi sahun mutanen da suka hadu da fushin hukumar tsaro ta farin kaya a kasar SSS.

Rahotannin sun ce jami'an hukumar ta SSS sun kai samamen ne da marecen ranar Alhamis, inda suka bukaci sojojin dake gadin gidan sa a Abuja da su basu wuri su yi abinda ya kai su.

A cewar rahotannin, jami'an hukumar sun ce sun je gidan ne domin su samu ganawa da Kanar Sambo Dasuki dangane da wasu lamura, inda har su ka yi barazanar kutsawa cikin gidan da karfi idan aka ki basu hadin kai.

Kawo yanzu dai babu wata hukuma ta gwamnati data fito fili ta ce wani abu dangane da wannan kawanya, amma wata majiya ta tabbatar wa BBC wannan lamari.