Yau take Sallah

Image caption Ranar Jumu'ah za a soma bukukuwan karamar sallah

A Najeriya Sarkin musulmi Muhammadi Sa'ad Abubakar ya bayyyana Jumu'ah, 17 ga watan Yuli a matsayin ranar karamar sallah, abin da ya kawo karshen azumin watan Ramadan.

Hakan na nufin musulmi a Najeriya za su bi sahun 'yan uwansu a wurare daban-daban na duniya wajen gudanar da bukukuwan karamar sallah.

Sarkin musulmin ya ce an ga sabon watan na Shawwal a jihohi 10 na kasar.

Tuni dai gwamnatin Nigeria ta ayyana Jumu'ah da Litinin a matsayin ranakun hutu.