An kashe kwamandojin al-Shabab

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mayakan kungiyar al-Shabab

Rundunar sojin Somalia ta ce ta yi amannar an hallaka wasu shugabannin kungiyar masu kaifin Kishin Islama su biyu a wani hari da wani jirgin da ba matuki ya kai a kudancin kasar.

Mutanen da ke kusa da garin Baardheere a yankin Gedo, sun ce sun ji karar fashewar a wani abu da asubahin ranar Alhamis.

Daga nan ne kuma mayakan kungiyar Al-Shabaab suka garzaya wurin da abun ya faru.

Garin na Baardheere na daga cikin kadan din da suka rage a hannun kungiyar Al-Shabaab, sai dai sojojin kungiyar kasashen Afrika da na gwamnatin Somaliyar suna dannawa yankin.

A cikin 'yan shekarun nan dai, hare-haren da Amurka ke kai wa da jiragen da babu matuki sun yi sanadiyyar hallaka shugabannin kungiyar Al-Shabaab da dama.