Jami'an tsohuwar gwamnatin Yemen sun koma kasar

Hakkin mallakar hoto
Image caption An fatattaki 'yan tawaye daga birnin Aden

An bada rahotan cewa Ministoci da dama da kuma manyan jami'an leken asirin gwamnatin Yemen dake gudun hijira sun sauka a birnin Aden na kudancin kasar

Kamfanin dilacin Labaru na Reuters ya ce sun sauka ne daga jirgin helicopta a ziyararsu ta farko cikin fiye da watanni uku na yakin da ake yi a cikin kasar

Sun kasance a kasar Saudiyya tun lokacin da aka tilastawa Shugaba Abd Mansur Hadi barin Yemen din a cikin watan Maris, bayan da 'yan tawayen Houthi dake samun goyan bayan Iran suka kwace wasu yankuna na Kasar

Mayakan dake samun goyan bayan hare- haren saman da kasar Saudiyya ke jagoranta sun fatattaki 'yan tawayen daga birnin na Aden a wani farmaki da aka kaddamar a ranar Talata