Hukumomi sun damke mabarata a Edo

Hakkin mallakar hoto edo govt
Image caption Gwamna Adams Oshiomole na Edo

Gwamnatin jihar Edo da ke kudancin Nigeria ta tsare daruruwan mabarata wadanda ta damke su a kan titunan Benin babban birnin jihar.

Tun daga ranar Litinin gwamnatin ta soma kai samamen inda ta kama yara da kuma nakasassu tsofaffi ciki har da makafi da guragu.

Galibin mabaratan 'yan asalin jihohin arewacin kasar ne.

BBC ta tuntubi kwamishiniyar harkokin mata da walwalar jama'a amma kawo yanzu ba ta ce komai a kan batun ba.

A makonnin da suka wuce ne gwamnatin jihar Kaduna ta haramta bara da talla a kan titi saboda dalilan tsaro.